Tsohon Sanatan Katsina ya mutu yana da shekara 62

Bello Mandiya

Tsohon Sanata da ya wakilci yankin Katsina ta Kudu, Bello Mandiya, ya rasu yana da shekara 62 a duniya.

Mandiya ya rasu a ranar Litinin, 7 ga Satumba, 2026, a cewar wata sanarwa da Ibrahim Mohammed, Mai Magana da Yawun Gwamnan Jihar Katsina Dikko Radda, ya fitar.

Radda ya bayyana kaduwarsa da bakin ciki kan rasuwar, inda ya ce babban rashi ne ga Jihar Katsina da Najeriya baki daya.

“Labarin rasuwar Sanata Bello Mandiya ya zo min cikin kaduwa da bakin ciki. Rasuwarsa babban rashi ne ga Jihar Katsina da Najeriya,” in ji gwamnan.

Radda ya bayyana Mandiya a matsayin babban ma’aikacin gwamnati mai jajircewa wanda ya ba da gudunmawa wajen cigaban Jihar Katsina da Najeriya.

“Sanata Mandiya ya sadaukar da wani bangare na rayuwarsa wajen hidimar kasa, ya kuma yi wa mutanen mu hidima da jajircewa. Gudunmawar sa zata ci gaba da zama abar tunawa,” in ji shi.

A cewar gwamnan, Mandiya ya taba zama Shugaban Ma’aikata ga tsohon Gwamnan Jihar Katsina Aminu Bello Masari kafin a zabe shi a matsayin Sanata, inda ya wakilci Katsina ta Kudu daga 2019 zuwa 2023.

“Kwarewa da hidimarsa a matakin jiha da na tarayya wani bangare ne na gadon da ya bari,” in ji Radda.

Gwamnan ya mika sakon ta’aziyya ga iyalan Mandiya, tsohon Gwamna Masari, al’ummar Katsina ta Kudu, abokan huldar siyasarsa da abokansa da kuma abokan aikinsa na Majalisar Dattawa ta 9.

“Ina rokon Allah Madaukakin Sarki ya gafarta masa kura-kuransa, ya saka masa da ayyukansa na alkhairi, ya kuma ba shi Aljannatul Firdaus. Allah ya ba iyalansa da masoyansa hakurin jure wannan rashi mai zafi,” in ji Radda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here