Wani jirgin jigilar Alhazan Najeriya da Saudiyya ta ayyana, Flynas, ya rattaba hannu kan yarjejeniyar jigilar alhazai da gwamnatin Najeriya domin gudanar da ayyukan Hajji na shekarar 2025.
Hakan na zuwa ne bayan Najeriya ta sanar da fara jigilar maniyyatan ta zuwa Saudiyya a ranar 5 ga Mayu, 2025.
Babban jami’in kasuwanci na Flynas, Khaled Alhejairi, da shugaban hukumar alhazai ta kasa (NAHCON), Farfesa Abdullahi Saleh Usman, ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar jigilar alhazai ta 2025 a ranar Litinin a hedikwatar hukumar da ke Abuja.
An rattaba hannu kan yarjejeniyar ne a gaban Daraktan cigaban kasuwanci na Flynas, Yasser Ajlan, da Manajan Bunkasa Kasuwanci, Hani Isma’il, da Manajan Daraktan kamfanin First Planet Travels and General Sales Agent (GSA) na Flynas a Najeriya, Alhaji Umar Kaila.
Karanta: Hukumar NAHCON ta amince da yin rijistar aikin Hajji a lokacin azumin Ramadan
Alhejairi ya yi alkawarin dorewar kyakkyawan aikin kamfanin su na samar da ayyuka masu inganci ga mahajjatan Najeriya.
A farkon watan Janairu, Hukumar Alhazan ta amince da Flynas da wasu jirage 3 da suka haɗar da Air Peace, Max Air, da Umza Aviation Services Limited don gudanar da aikin Hajjin 2025.
Hukumar alhazai ta Najeriya ta ce tun farko ta ware maniyata 71,274 a matsayin maniyyatan da za su bi jirgin Flynas zuwa kasar Saudiyya, sai maniyyata 9,145 ga Air Peace, da maniyyata 23,342 zuwa ga Max Air, sai kuma maniyyata 15,893 zuwa Umza Air.