Hukumar Ƴan sanda ta ƙasa ta amince da naɗin CP Ibrahim Adamu Bakori a matsayin sabon kwamishinan ƴan sandan jihar Kano, inda zai maye gurbin CP Salman Garba Dogo wanda ya samu ƙarin girma zuwa mataimakin sifeto janar na ƙasa (AIG).
Kafin naɗin nasa, CP Bakori ya kasance kwamishinan ƴansanda mai kula da sashen binciken kisan jama’a a hedikwatar ƴansandan ƙasa da ke Abuja.
Shugaban hukumar ƴan sandan, DIG Hashimu Argungu mai ritaya ya nemi sabon kwamishinan na Kano da ya tabbatar an samu zaman lafiya mai ɗorewa a jihar.
Karin karatu: Majalisar Wakilai ta umarci hukumar sadarwa NCC ta rufe duk wasu shafukan batsa na intanet
Ya ƙara da cewa ya yi ƙoƙarin wajen tunkarar ƙalubalen da ke gabansa wajen tabbatar da an daƙile ƙaruwar aikata laifuka a jihar mai yawan jama’a.
Jihar Kano dai na fama da matsalolin dabanci da ƙwacen waya da sace-sace da kuma a baya-bayan nan rikicin masarautar Kano da ya janyo al’umma suka sauya tunaninsu kan rundunar ƴansandan jihar.













































