Hukumar NAFDAC ta kwace magungunan kara karfin maza wanda basu da rijista a Kaduna

Nafdac gg
Nafdac gg

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa (NAFDAC) a ranar litinin ta bayyana cewa ta kama wasu nau’ukan kara karfin maza da ba a yi musu rijista ba a Kaduna.

Solacebase ta ruwaito cewa aphrodisiac wani nau’in magani ne wanda ke haifar da sha’awar jima’i, yana kawo sha’awa, ko ƙara jin daɗin jima’i.

Shugaban hukumar ta NAFDAC a jihar Kaduna, Malam Nasiru Mato, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN cewa an kama su ne daga samamen aka gudanar domin kawar da kayayyakin da ba a kayyade ba a jihar.

Ya bayyana sunan wasu daga cikin kayayyakin da aka kama wanda suka hada da: Power Coffee, Honeymoon, Viga 150000, Zahidi Coffee da Big Boss.

“NAFDAC ta yawan wayar da kan al’umma kan illolin da ke tattare da amfani da irin wadannan kayayyakin, wanda suke haifar da gagarumar matsala ga lafiyar al’umma.

“Suna iya lalata muhimman gabobin jiki. Magungunan suna sa zuciya ta yi aikin da ya fi karfinta, wanda  hakan ke iya haifar da hauhawar jini da mutuwar ba zata.

Mato ya ba da shawarar cewa mutane su dai daina amfani da magungunan kara karfi ba tare da izinin likita ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here