Majalisar wakilai ta umarci hukumar sadarwa ta ƙasa NCC da ta umurci kamfanonin da ke wallafa hotuna ko bidiyo na batsa a intanet su rufe duk wasushafukansu cikin gaggawa.
Majalisar ta cimma matsayar ne bayan wani ƙudiri da ɗan majalisa daga jihar Katsina, Dalhatu Tafoki, ya gabatar.
Tafoki ya bayyana cewa bidiyoyin batsa da ke intanet na zama babbar matsala a duniya, kuma zuwa yanzu Najeriya ba ta ɗauki wani matakin magance matsalar ba.
Ya ce Najeriya ƙasa ce ta addini, inda manyan addinan ƙasar suka haramta batsa da kuma nuna tsiraici.
Karanta: Majalisar wakilai ta buƙaci a dakatar da ƙarin ƙudin cirar kuɗi a ATM
Ɗanmajalisar ya kuma bayyana gargaɗin da masana halayyar ɗan’adam suka yi kan mummunan tasirin da kallon bidiyon batsa ke da shi, ciki har da yiwuwar karfafa yin zina, da karuwanci, da kuma kasa rabuwa da kallon ta.
Majalisar ta kuma buƙaci hukumar NCC ta hukunta duk kamfanin da ke Irin wannan aiki a intanet idan ya ƙi bin umarnin.