Shugaban hukumar kula da jin daɗin alhazan Kano ya yi murabus daga muƙamin sa

Rabiu

Babban daraktan hukumar kula da jin daɗin alhazan Jihar Kano, Alhaji Laminu Rabiu, ya yi murabus daga mukaminsa nan take.

Takardar murabus ɗin na ɗauke da kwanan wata 25 ga Janairu 2026, kuma an miƙa ta ga gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf.

A cikin takardar, Laminu Rabiu ya nuna cewa matakin da ya ɗauka ya samo asali ne daga abubuwan siyasa da suka faru a baya-bayan nan a jihar.

Ya bayyana cewa sauye-sauyen siyasar da ake fuskanta sun shafi yanayin aikinsa da matsayinsa a halin yanzu.

Wannan yanayi ya sanya dole ya sake tsara hankalinsa da alkiblar jajircewarsa.

Saboda haka, ya yanke shawarar barin muƙaminsa domin mayar da hankali kan sabon yanayi da ya taso.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here