Gobara ta kone gidan Kwamishinan Harkokin Gona na Jihar Ogun a ranar Alhamis.
Iftila’in ya faru ne a yankin Kemta Idi-Aba da ke Abeokuta, babban birnin jihar.
Ya zuwa hada wannan labari ba a samu cikakken bayani ba kan dalilin aukuwar gobarar.
Kwamishinan, Dokta Odedina shi ne wanda ya tabbatar da aukuwar gobarar, inda ya ce babu wanda ya rasa ransa a musibar da ta auku.
Daraktan Hukumar Kwana-kwana na Jihar Ogun, ya ce da alama wutar ta samo tushe ne daga dakin girke-girke na gidan.













































