Yan Bindiga Sun Sace Daliban Firamaren Gwamnati a Jihar Nasarawa 

cb00962dc9736047
cb00962dc9736047

Wasu tsagerun ‘yan bindiga sun sanyin safiyar ranar Juma’a sun kai mummunan hari makarantar Firamaren Gwamnati da ke Alwaza a karamar hukumar Doma a jihar Nasarawa.

Ana zargin ‘yan bindigan sun yi awon gaba da wani adadi na dalibai na makarantar, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito. An ce ‘yan bindigan sun saraf sun sace daliban ne da safe a daidai lokacin da suke zuwa makarantar da safe.

Ya zuwa yanzu dai ba a san inda ‘yan bindigan suka yi da daliban ba, kamar yadda rahoton jaridar Punch ya bayyana.

Da aka tuntube shi, kakakin rundunar ‘yan sandan jihar DSP Rahman Nansel ya tabbatar da faruwar lamarin. A cewar rundunar ‘yan sanda, gamayyar rundunar tsaro ta ‘yan sanda, sojoji da ‘yan banga na ci gaba da sintiri don gano inda ‘yan bindigan suka shiga.

Ba wannan ne karon farko da ake sace dalibai ba a Najeriya, hakan ya sha faruwa a yankuna daban-daban na Arewacin kasar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here