Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai bar Abuja ranar Asabar don kai ziyarar aiki a kasashen Faransa, Kenya da Ruwanda.
A sanarwa da mai baiwa Shugaban Kasa Shawara na Musamman kan Harkokin Yada Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Juma’a, tafiyar za ta fara da Faransa kafin shugaban ya wuce Nairobi, Kenya.
Ana sa ran Tinubu zai halarci Taron Afrika da Faransa a Nairobi, wanda Emmanuel Macron da William Ruto za su jagoranta tare.
Taron, wanda aka shirya yi daga 11 zuwa 12 ga Mayu, zai mayar da hankali kan batutuwa da suka hada da makamashi, fasahar zamani da daukar mataki kan sauyin yanayi.
“Halartar Shugaba Tinubu taron daga 11 zuwa 12 ga Mayu zai maida hankali kan jajircewar Najeriya a bangaren karfafa hadin gwiwa da dabaru kan kasashen Afrika da kasar Faransa,” in ji sanarwar.
Bayan taron na Kenya, Shugaban kasa zai wuce Kigali, Ruwanda, don halartar Taron Shugabannin Kamfanoni na Afrika da za a yi daga 14 zuwa 15 ga Mayu.
Sanarwar ta kuma cewa taron, wanda aka shirya hadin gwiwa da Hukumar Kudi ta Duniya (IFC), zai hada shugabannin kasuwanci da masu tsara manufofi don tattauna bunkasar tattalin arziki da zuba jari a fadin nahiyar.
“A duka tarukan biyu, Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi wanda zai nuna irin sauye-sauyen da gwamnatinsa ke ci gaba da yi don mayar da kasar wuri mai jan hankali ga masu zuba jari da ci gaba.
Sanarwar ta kara da cewa shugaban zai gudanar da manyan tarurruka da manyan shugabannin kasuwanci na duniya da na Afrika. Inda ta kuma tabbatar da cewa shugaban zai samu rakiyar wasu daga cikin ministocinsa da manyan hadimansa.
Ana sa ran zai dawo Najeriya bayan kammala taron na Ruwanda.












































