An yi wani abu mai kama da wasan kwaikwayo a hedikwatar rundunar ‘yan sandan jihar Kano lokacin da Fatima Maina, mahaifiyar Hanifa Abubakar, dalibar ‘yar shekara 5 da aka yi garkuwa da ita a hanyarta ta zuwa makarantar Islamiyya a watan Disamba ta hango wanda yake kashe ‘yarta.
A yau Juma’a ne, iyayen yarinyar da aka kashe da wadanda ake zargin suka. Bayyana a hedikwatar ‘yan sandan Kano.
Iyayen yarinyar su ne suka fara isa wurin sai Daga baya sai ‘yan sanda suka kawo Tanko da wadanda ake zargin.
Nan take Fatima ta hango Tanko, sai ta afka kan sa da mari da duka , yayin da take dalilin da ya sa ya kashe diyarta.
An yi tata burza na tsahon lokaci, har sai da ‘yan sanda suka dauke wanda ake zargin.
A lokacin da aka gabatar da shi a hedikwatar ‘yan sandan Kano a ranar Juma’a, ya shaida wa manema labarai cewa ya sanya wa yarinyar guba da gubar bera da ya saya a kan Naira 100.
An kama Abdulmalik Tanko, mai makarantar Noble Kids Academy, Kawarna Dakata, Kano, dangane da zargin garkuwa da Hanifa tare da kashe ta.
Tun a watan Disamba ne aka yi garkuwa da ita, kuma masu garkuwa da ita sun bukaci a biya ta Naira miliyan 6.
Yayin da ake kokarin karbar wani bangare na kudin fansa, jami’an tsaro sun cafke Tanko da wasu da ake zargi.













































