Wani dan gwagwarmaya ya maka gwamnatin tarayya a gaban kotu kan hakar ma’adanai a Kano

Court High
Court High

Wani dan gwagwarmayar kare muhalli , Dazumi Mohammed ya garzaya wata babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano karkashin jagorancin mai shari’a A M Liman yana neman da ta dakatar da gwamnatin tarayya da kamfanonin fasa kwal da ke aiki a karamar hukumar Kumbotso daga ayyukan hakar man ma’adanai.

Solacebase ta bada rahoton cewa mai karar ya bayyana cewa ayyukan kamfanonin hakar na zama hadari ga rayuwar wadanda ke zaune a yankunan da suke gudanar da ayyukansu.

Ya shaida wa kotun cewa ayyukan wadanda ake kara sun hada da illar lafiya ga rayuka da dukiyoyin wadanda ke zaune a yankunan, inda suke gudanar da ayyukansu.

Wanda ya shigar da karar ta bakin lauyansa Barista Abdulrazak .S. Aikawa a ranar Alhamis ya roki kotu da ta bayyana ayyukan duk wadanda ke da alaka da sana’ar fasa dutse a kauyen Danjirma da ke karamar hukumar Kumbotso a jihar Kano a matsayin aikin da bai kamata ba.

Ya bukaci kotun da ta umarci ministan ma’adinai da karafa,  Salisu S.Wali, wanda shi ne jami’in lasisin hakar ma’adanai a Kano, Ahmad Musa, babban lauyan gwamnatin tarayya kuma ministan shari’a da su daina ayyukan hakar ma’adanai a yankin.

Kotun ta dage sauraron karar zuwa ranar 2 ga Fabrairu, 2022, don sauraron umarnin shiga tsakani.

Kotun ta kara da ba da umarnin cewa ya kamata a kammala dukkan matakai kafin ranar da aka dage.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here