AMCON ta karbe kamfanin rarraba wutar lantarki

Hukumar Kula da Kaddarorin gwamnatin Najeriya AMCON ta karbe ikon Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Ibadan IBEDC.

Babban jami’in gudanarwa na kamfanin, John Ayodele, ne ya sanar da ma’aikatan cewa sun karbe Disco din a ranar 20 ga Janairu, 2022.

A cewar sanarwar ta bayyana cewa kamfanin bai ya kasa biyan bashin da ake binsa  don haka aka kwace.

Lamarin ya janyo firgici a tsakanin ma’aikatan, amma babban jami’in gudanarwa ya tabbatar musu da cewa an ayyukan su ba zasu shiga matsala ba.

Wani ma’aikacin kamfanin da ya nemi a sunansa shi ma ya tabbatar wa Solacebase ci gaban a ranar Juma’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here