Kungiyar ‘yan Fansho ta kasa ta yi barazanar gudanar da zanga-zanga a jihohin da gwamnoni suka ki cika alkawarin da suka dauka na biyan bashin da ‘yan fansho ke bi.
Shugaban Kungiyar Goodwin Abumisi ne ya bayyana hakan a wajen taron ranar ‘yan fansho ta duniya wanda aka gudanar jiya Lahadi a Abuja.
Ya ce matukar gwamnoni suna so a zauna lafiya da su to dole ne su biya bashin da ‘yan fansho ke bin su, sannan su ringa biyan ‘yan fansho hakkin su ko wane wata.
Ya kara da cewa babbar matsalar da suke fuskanta da gwamnoni ne, sune basa daukar lamarin ‘yan fansho da muhimmanci, wanda hakan ya sanya basa biyan su hakkokin su akan lokaci.
Goodwin Abumisi ya bukaci jihohin da suke da matsala da ‘yan fansho da su yi gaggawar magance matsalolin, idan ba haka ba zasu fara gudanar da zanga-zanga.













































