Sarkin Daura ya nada Yusuf Buhari a matsayin Hakimi

07175FEE D886 4252 8BF0 D1DD13E19598
07175FEE D886 4252 8BF0 D1DD13E19598

A yau asabar ne aka yi bikin nada dan Shugaban Nigeria Muhammadu Buhari wato Yusuf Buhari a matsayin Talban Daura kuma Hakimin Kwasarawa.

Sarkin Daura Alhaji Umar Farouk shine ya nada Yusuf Buhari wannan sarautar bisa irin gudunmawar da yake bawa masarautar.

Bikin nadin sarautar ya samu halartar Mataimakin Sugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo da Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya Ahmad Lawan da sauran manyan baki wanda suka hada da gwamnan Katsina Aminu Bello Masari da Gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje da Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero.

An gudanar da wannan bikin ne a yayin da shugaban Najeriyar ke Turkiyya inda yake halartar taron cinikayya tsakanin Turkiyya da Afrika.

A yan watannin da suka gabata ne sabon Talban Daura Yusuf Muhammadu Buhari ya auri ‘yar Gidan Sarki Bichi Zahra Nasir Ado Bayero.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here