Jihar Nasarawa ta haramta amfani da Gawayi

B79B3680 E315 486E 88D2 1F5EDE74A4B8
B79B3680 E315 486E 88D2 1F5EDE74A4B8

Gwamnatin jihar Nasarawa ta haramta yin amfani da gawayi a ciki da wajen jihar domin kare muhalli.

Babban sakataren ma’aikatar Muhalli na jihar Aliyu Agwai, shine ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai yau a Asabar a Lafia babban birnin.

Ya ce an dauki wannan mataki ne domin kare jihar daga gurbatar yanayi tare da dumamar yanayi.

Ya kara da cewa amfani da gawayi yana kara ta’azzara zafi a cikin jihar.

Ya bukaci masu amfani tare da siyar da Gawayi da su kujewa amfani da Gawayin domin kaucewa kaucewa fishin hukuma.

Ya yabawa al’ummar jihar bisa yadda suke biyayya ga gwamnati musamman ma kan dokokin muhalli.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here