Tsohon shugaban majalisar dattawa kuma Wazirin masarautar Ilorin, Dakta Abubakar Bukola Saraki, ya yi kira da a gudanar da bincike a fili kan zarge-zarge da cin zarafi da kuma rashin mutunta dokokin majalisar dattawa da ke faruwa tsakanin shugaban majalisar fattawa, Godswill Akpabio da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Saraki, wanda ya kasance shugaban majalisar dattawa ta 8 tsakanin 2015 -2019, ya bayyana cewa binciken ya zama dole domin gano gaskiya da kuma kare mutuncin majalisar a matsayin ta na hukuma.
Karin karatu: Akpabio ya so ya kwanta da ni kafin ya bar ni in gabatar da ƙudiri – Natasha
A wani dogon rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Asabar da yamma, tsohon gwamnan jihar Kwara kuma jigo a jam’iyyar adawa ta PDP, ya bukaci majalisar dattawa ta 10 ta gabatar da Akpabio da Natasha don gudanar da bincike na gaskiya domin a gano tushen lamarin, inda ya kara da cewa irin wannan lamari ya taba faruwa lokacin da yake shugaban majalisar dattawa.