
Sojojin Najeriya sun tabbatar da mutuwar mutum 30 a wata arangama tsakanin wasu ƙungiyoyin ‘yan tayar da ƙayar baya a yankin ƙaramar hukumar Ukum da ke jihar Benue, inda sojojin suka musanta batun cewa kashe-kashen na da alaƙa da rikicin makiyaya.
Babban kwamandan ‘Operation Whirl Stroke’ kuma shugaban kwamitin tabbatar da aiki da dokar hana kiwon sake a jihar, Manjo Janar Sunday Igbinomwanhia ne ya bayyana haka a wani taron manema labarai da ya gudanar ranar Laraba yayin da jihar ta fara aiwatar da dokar hana kiwon sake, bayan cikar wa’adin mako biyu da jihar ta bayar.
Karin labari: Yadda ‘yan bindiga suka kashe makiyaya da shanu 35 a jihar Filato
Yayin da yake tabbatar da kasashe-kashen na Ukum, Manjo Igbinomwanhia ya ce aikin wanzar da zaman lafiya da sojoji ke yi a ƙaramar hukumar Kwande ya taimaka wajen daidaita al’amura a yankin bayan kashe aƙalla mutum 27 a yankin mako biyu da suka gabata.
Jihar Benue da ke yankin tsakiyar Najeriya na daga cikin jihohin ƙasar da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga masu ɗauke da makamai da ke da alaƙa da ƙabilanci da addini da rikicin manoma da makiyaya.












































