‘Yan sanda sun kama mutum 254 bisa zargin garkuwa a Najeriya

'Yan sandan, Najeriya, kama, mutane, najeriya
Rundunar 'yan sanda Najeriya ta ce ta kama mutum 254 cikin mako biyu da take zargi da aikata miyagun laifuka a faɗin. Cikin wata sanarwar da kakakin rundunar...

Rundunar ‘yan sanda Najeriya ta ce ta kama mutum 254 cikin mako biyu da take zargi da aikata miyagun laifuka a faɗin.

Cikin wata sanarwar da kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ya fitar ya ce rundunar ta samu gagarumin cigaba a yaƙi da aikata miyagun laifuka a faɗin ƙasar.

Karin labari: “Mutum 30 ne suka mutu a arangamar kungiyoyi masu makamai a Benue” – Sojoji

”Bisa koƙarin da rundunar ‘yan sada ta yi ta samu nasara kama mutum 254 da take zargi da aikata laifuka ciki har da ‘yan fashi 92 da masu garkuwa da mutane 153 tare da mutum tara da ake zargi da aiki da ƙungiyoyin asiri” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ce ‘yan sandan sun kuma kuɓutar da mutum 35 da aka yi garkuwa da su, tare da ƙwato ababen hawa bakwai da aka sace.

Karin labari: Gwamnatin Kano ta karyata barkewar cutar kyanda

Haka kuma ‘yan sandan sun kuma ce sun ƙwato bindigogi 44 tare da harsasai kusan 477 da bindigogi daban-daban.

Rundunar ‘yan sanda ta ce ta ƙaddamar da samamen ne a jihohin Plateau da Cross River da Taraba da kuma birnin tarayyar Abuja.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here