Gwamnatin tarayya ta dakile Masu Samar da gurbataccen Taki

images 1 10
images 1 10

Gwamnatin tarayya ta ce ta dakile gurbatattun taki a jihar Kano domin tabbatar da samar da ingantaccen takin zamani da kayan amfanin gona.

Mataimakiyar babban jami’in yada labarai na ma’aikatar noma da raya karkara ta tarayya Anthonia Eremah, ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar ranar juma’a a Abuja.

Ta ce hakan ya yi daidai da kudurin gwamnati na tabbatar da samar da taki mai inganci da kayan amfanin gona da aka tsara domin samun nasarar samar da abinci mai gina jiki.

Eremah, ta bayyana cewa, tawagar ma’aikatar karkashin jagorancin Daraktan Sashen bunkasa tallafin kayan aikin gona (FISSD), Mista Kwaido Sanni, tare da jami’an ‘yan sanda da kuma jami’an DSS sun shiga aikin rufe haramtattun kayayyakin a Kano.

Ta ce atisayen wanda ya gudana a ranakun 17 da 18 ga watan Agustan da muke ciki a kananan hukumomi daban-daban, ya kasance cikamakin ka’idojin kula da ingancin taki na kasa na shekarar 2020, sashe na 43, karamin sashe na 1 na kundin tsarin mulkin kasa.

Ta ce kundin tsarin mulkin kasar ya baiwa hukumar ta FISSD damar kawar da duk wata al’mundahana a bangaren samar da taki.

Sanni, ya bayyana cewa dokar hana takin zamani za ta tabbatar da cewa duk wani mai sana’ar dole ne ya yi rajista da hukumar ta FISSD tare da mallakar kayayyakin da ake bukata don gudanar da ayyukansa a bangaren.

Ya ce yawancin kamfanonin taki ba sa son gudanar da aikin ne saboda sun san ba su cancanta ba.

Daraktan ya ce hakan ne ya sa aka dakatar da kamfanonin.

Don haka ya gargadi masu gudanar da wannan sana’ar da su daina gudanar da it aba bisa ka’ida ba ko kuma su fuskanci fushin doka.

Jami’in kula da ingancin takin zamani, (FISSD), Mista Sunday Oke, a yayin ziyarar, ya lura da yadda gurbatattun takin zamani ke yaduwa a jihar.

Oke, ya ce za a tattara samfuran takin a kai su Abuja don gudanar da bincike a dakin gwaje-gwaje da nufin tabbatar da ingancinsu.

Ya ce atisayen na yini na biyu ya shafi karkatar da kayayyakin da gwamnati ta siyo.

Ya ce akwai wani tanadi a dokar da ya bayyana cewa karkatar da takin laifi ne.
“Wannan shi ne dalilin da ya sa muka je kasuwa muka ga irin kayayyakin da ake sayar da su a kasuwannin bayan fage” in ji shi.

Ya bayyana cewa an yi amfani da takin ne domin hada takin NPK na cikin gida a kasar nan, yana mai cewa hakan ya sabawa dokar.

Shugaban Kasuwar ‘Yandusa ta Kano, Alhaji Shehu Akarami, a yayin ziyarar ya bayyana cewa ya shafe shekaru 40 yana sana’ar takin zamani kuma yana bukatar tallafin Gwamnatin Tarayya domin bunkasa kasuwancinsa.

Daya daga cikin wadanda suka gaza, Malam Khalid Mohammed, dake shago mai lamba 18, Dogon-Gida a Kasuwar Sabon Gari, ta Kano, inda aka gano buhunan PTF kusan 800, sai dai ya ce bai da masaniyar lamarin cewa kuskure ne sayar da takin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here