Kano ta shirya zaben kananan hukumomi bayan kotun Kano ta baiwa KANSIEC damar gudanar da zaben

download

Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jihar Kano (KANSIEC) ta tabbatar da shirinta na gudanar da zaben kananan hukumomi da aka tsara a ranar Asabar, 26 ga Oktoba, 2024.

Shugaban KANSIEC, Farfesa Sani Malumfashi, ya bayyana hakan a ranar Juma’a, bayan Kotun Kolin Jihar Kano ta yanke hukunci a madadin hukumar, wanda ya rushe hukuncin wata kotun tarayya da ta dakatar da zaben.

Alkalin babbar kotun tarayya, Simon Amobeda, a baya ya yanke hukunci na hana gudanar da zaben, tare da cire Malumfashi da wasu mambobi biyar na hukumar.

Sai dai, hukuncin babbar kotun yanzu ya ba da damar ci gaba da zaben kamar yadda aka tsara.

Farfesa Malumfashi ya ce an tsara matakan tsaro tare da hadin gwiwar ‘yan sanda don tabbatar da kwanciyar hankali yayin zaben.

Shugaban hukumar ya bayyana rashin jin dadinsa kan rashin shiga zaben da wani jam’iyya ta yi, inda ya ce jam’iyyar ta gaza cika lokutan da aka diba na gabatar da ‘yan takara da sayen fom.

Ya bayyana cewa duk sauran jam’iyyu kamar su NNPP, ZLP, Accord Party, NRM, AAC, da AA sun shiga cikin shirye-shiryen gudanar da zaben.

Malumfashi ya jaddada aniyar jihar na gudanar da zabe mai gaskiya da adalci, kamar yadda gwamnatin tarayya ta umarta a kammala kafin Oktoba 2024.

Ya bukaci duk masu ruwa da tsaki su goyi bayan tsarin, yana mai jaddada kudurin KANSIEC na bi doka da oda a duk shirin zaben, gami da zaben kwamishinoni da Majalisar Dokokin Jiha ta amince da su.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here