A yau Asabar 20 ga watan Agusta ne rundunar ‘yan sandan jihar Osun ta tabbatar da an kai farmaki kan ayarin motocin uwar gidan gwamnan jihar, Misis Kafayat Oyetola a jiya Juma’a a Owode na yankin Ede.
Rahotanni a baya sun bayyana yadda wasu matasa suka yi wa ayarin uwar gidan gwamna ba dadi.
Sannan kuma rundunar ta ‘yan sandan ta tabbatar da kame wasu mutane biyar da ake zargi da hannu a farmakar tawagar uwar gidan gwamnan.













































