Farfesa ‘yar Najeriyar nan dake zaune a Amurka da ta yi fatan mutuwa mai radadi ga sarauniyar Ingila ta bayyana cewa, rayuwarta na cikin matsanancin hali. Uju Anya farfesa ce a sashen Harsunan Zamani a Jami’ar Carnegie Mellon ta kasar Amurka, in ji jaridar The Punch.
Farfesar ta jawo cece-kuce a kafar sada zumunta ta Twitter a ranar da aka sanar da cewa sarauniyar Ingila na can kwance jina-jina a asibiti.
A wani rubutu da ta yi a Twitter, ta bayyana cewa, tana fatan sarauniya Elizabeth II ta yi mummunan mutuwa saboda wasu dalilai da ta bayyana. Wannan magana ta jawo maganganu daga bangarori daban-daban a duniya, ciki har da fitattun ‘yan kasuwa irinsu Jeff Bezos; mai kamfanin Amazon.
Ta zargi cewa, mai kamfanin na Amazon ya jawo jama’a suna ta yi mata barazana daga bangarori daban-daban na duniya, Pulse ta ruwaito.
Ta bayyana cewa: “Ina jin kamar rayuwata na cikin hadari. Ba na samun natsuwa da kwanciyar hankali bisa wadannan karairayi da lika min.. Na bar amfani Facebook shekaru hudu da suka gabata.”
Ta kuma koka da yadda ake ta’allaka ta da kungiyar nan ta ta’addanci wato IPOB, inda tace sam bata da alaka dasu.











































