Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sake kai ziyara Jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar don kaddamar da wasu ayyukan da gwamnatin Jihar ta kammala, duk da barazanar ‘yan aware.
Wannan na zuwa ne bayyan kungiyar fafutukar kafa kasar Biafra ta IPOB ta ayyana dokar zaman gida a Jihar ta Imo da ma yankin baki daya, don bada hadin kai ga shugabanta Mazi Nnamdi Kanu wanda ya sake bayyana a kotu jiya.
Amma duk da hakan, wasu kungiyoyi da wasu mutane sun fito tarbar shugaban kasar, ciki har da kungiyar kare muradun kabilar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo.
Dakta Alex Ogbonnia da ke kakakin kungiyar Ohanaeze Ndigbo ya ce sun zo Jihar Imo a wannan zuwan na shugaba Buhari ne don wasu dalilai biyu.
Ya ce, “Daya daga cikin dabi’un gargajiya na kabilar Igbo shi ne idan mutum ya zo gurinka ka yi mishi marhaban, a kowane irin halin da ku ke da shi. Na biyu kuma shi ne muna ganin wannan ziyarar ta shugaba Buhari Imo wata dama ce ta tunatar da shi cewa har yanzu ‘yan kabilar Igbo na bukatar sakin Nnamdi Kanu. Kuma za mu sake mika masa wannan sakon.”












































