Ba don ni ba da Buhari bai zama Shugaban Kasa a shekarar 2015 ba-Tinubu

Tinubu speaking
Tinubu speaking

Mai neman takarar kujerar shugabancin kasar nan kuma jigo a jam’iyyar APC Bola Ahmad Tinubu, ya ce ba don shi ba da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari bai shugabanci kasar nan a shekarar 2015 ba.

Tinubu ya bayyana hakan ne a babban dakin taro dake birnin Abeokuta, yayin da yake yiwa wakilan jam’iyyar APC jawabi, akan zaben fidda gwanin Dan Takarar Shugabancin Kasa na Jam’iyyar da ake dab da gudanarwa.

Ya ce tunda Buhari ya hau karagar mulki ba’a ba shi Minista ba, balle wata kwangila.

Don haka wannan lokaci ne na Yarbawa da yankin su, Kuma shi ne mafi chanchanta ya shugabanci Kasar.

Jigon a jam’iyyar APC’n ya samu rakiyar gwamnan jahar Ogun Dapo Abiodun da na Lagos Babajide Sanwo-Olu, sai na Kano Abdullahi Umar Ganduje, da kuma tsohon gwamnan jihar Borno Sanata Kasim Shettima.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here