Tsohon Manajan Daraktan Banki ya shiga takarar tsayawa Gwamna a Zamfara

IMG 20220523 WA0142 678x381 1
IMG 20220523 WA0142 678x381 1

Dakta Dauda Lawan Dare, ya bayyana sha’awar sa ta shiga takarar neman kujerar gwamna Jihar Zamfara a babban zaben dake tafe.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da aka shirya masa gagarumar tarba, lokacin daya shiga Gusau Babban Birnin Jihar Zamfara daga Abuja.

Tsohon Darakta janar din na First Bank ya bayyana aniyar sa ta kokarin ceto Jihar idan ya kaiga samun nasara.

Anji lokacin da Dakta Dauda Lawan Dare, yake jaddada aniyarsa ta bada fifiko ga bangarorin inganta sha’anin tsaro, da habaka harkokin lafiya da ciyar da jama’a gaba, ta yadda Daukacin Al’ummar Jihar Zamfara za su yi gogayya da sauran takwarorin su dake fadin Najeriya.

Tsohon manajan daraktan bankin, ya koka ainun ganin yadda harkokin kasuwanci da zuba jari suka fadi kasa warwar a jihar Zamfara, yana mai cewa ya zame masa wajibi ya farfado da shi tare da inganta aikin gona a Jihar idan ya kai ga samun nasara.

“Ina kira ga dauka cin al’ummar wannan jiha tamu mai albarka dama kasa baki daya, cewa jama’a su garzaya su yanki katin kuri’a, domin da wannan ne kadai zasu sami sukunin zabar shugabanni da zasu ceto su daga kangin da aka jefa su a ciki”inji Dakta Dare.

A lokacin wannan gangami Dakta Dauda Lawan Dare, ya sami rakiyar kusoshin jama’iyar da wasu muhimman mutane irin su Hon. Ikira Aliyu Bilbis, tsohon shugaba hukumar lura da kafafen yada labarai ta kasa wato NBC, wanda yake neman kujerar Sanata a shiyya ta tsakiya da sauran muhimman mutane.

Sai dai kuma, tun da farko a jawabin daya gabatar, shugaban jam’iyyar PDP, kanal Bala Mande (mai ritaya) lokacin daya tarbi dan takarar cewa ya yi, ai ba wani kokwanto da yardar Allah, sune zasu lashe zabe a Jihar Zamfara, domin ganin irin dandazon bil-adam da suke musu dafifi a wannan lokaci da gwamnati bata hannun su kuma alama ce dake nuna cewa al’umma sun gaji da salon jagorancin gwamnati mai ci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here