Shugaban kasar Tunusiya Kais Saied, ya dakatar da alkalai 57 a ranar Laraba, bisa zargin cin hanci da rashawa da kuma ba da kariya ga ‘yan ta’adda”, yayin da yake neman sake fasalin tsarin siyasar kasar.
Wani fitacce da ake zargi shima yana da irin dabi’ar shi ne Bachir Akremi.
Wasu masu fafutuka a harkokin siyasa sun ce alkalin ya na da kusanci da jam’iyyar Ennahda kuma suna zarginsa da dakatar da kararrakin da ake yiwa Jam’iyyar.
Sai dai Ennahda da Akremi duk sun musanta zargin.
A watan Yulin da ya gabata ne, Saied ya kori mukarraban gwamnati tare da kwace ikon bangaren zartarwa, kafin daga bisani ya yi watsi da kundin tsarin mulkin kasar na 2014 tare da yin watsi da zababbun yan majalisar dokokin kasar.
Tun a wancan lokaci yake yanke hukunci bisa doka, yana mai cewa yana bukatar daukar matakin ceto kasar Tunisia daga rikicin da ta ke ciki.
Da farko dai yunkurin nasa ya nuna ya samu goyon bayan al’umma bayan shekaru da dama na tabarbarewar tattalin arziki da gurgunta harkokin siyasa da cin hanci da rashawa, amma hasarar rayukan Jama’a na karuwa yayin da hauhawar farashin kayayyaki da rashin aikin yi da kuma raguwar ayyukan gwamnati ke karuwa.
Saied, wanda kuma ya karbi ragamar hukumar zabe mai zaman kanta ta Kasar, ya ce zai gabatar da sabon kundin tsarin mulki a wannan watan da kuma ya sanya ta gudanar da zaben raba gardama a watan Yuli mai kamawa.
Sai dai kusan dukkanin jam’iyyun siyasar Tunisiya sun yi watsi da matakin tare da babbar kungiyar kwadago ta UGTT.
Kungiyar ta UGTT ta ce a ranar 16 ga Watan Yunin shekarar 2022 ma’aikatan gwamnati za su tsunduma yajin aiki, wanda ke zama babban kalubale kai tsaye ga kwace ikon Saied ya zuwa yanzu.













































