Sanarwar fadar
Shugaban kasa, “Zamu saki uwar kudi”…
Shugaban kasa Muhammadu Buhari, a karshen mako ya ba da tabbacin cewa gwamnati za ta tabbatar da cewa ‘yan kasa ba su sami wata matsala a harkokin kasuwanci ko samun cikas ga daukacin hanyoyin samar da kayayyaki da ke faruwa sakamakon musayar kudade.
Dayake maida martani kan dogayen layukan da jama’a ke yi na tsawon sa’o’i da dama suna jiran su ajiye tsofaffin takardun kudin su dan samun sababbi, lamarin ya janyo asara ga jama’a da shiga halin tsaka mai wuya.
Buhari ya kara da cewa an yi canjin kudin ne domin hana mutane jibge kudaden haram ba wai talaka ba. kuma ya zama dole a hana yin jabu, cin hanci da rashawa, da kudaden fansa da ‘yan ta’adda ke tattarawa. Ya kuma tabbatar da cewa hakan, zai daidaita tareda karfafa tattalin arzikin kasar.
An kuma lura da cewa al’umma mafiya talauci na fuskantar kunci domin a lokuta da dama suna jibge makudan kudade a gida don kashe kudade daban-daban.
Shugaba Buhari ya ba da tabbacin cewa gwamnati ba za ta bar su cikin halin da suke ciki ba.
Daganan ya nanata cewa akwai wasu tsare-tsare da babban bankin kasa da dukkan bankunan kasuwanci ke yi na gaggauta rarraba sabbin takardun kudi da kuma yin duk abin da ya dace don dakile kowanne irin hargitsi.
Garba Shehu
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa












































