Hukumar Yaki da masu yiwa tattalin arziki ta’annati (EFCC) ta tabbatar da sakin dakataccen tsohon Akanta Janar na Tarayya, Ahmed Idris, daga hannun ta.
Jami’in yada labaran hukumar Mista Wilson Uwujaren, shi ne ya tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN ranar Alhamis a Abuja, inda yace an saki Idris bayan cika sharuddan belin sa.
Hukumar ta EFCC ta kama tsohon Akantan ne a ranar 16 ga watan Mayun daya gabata bisa zargin karkatar da kudade da suka kai naira biliyan 80.
Hukumar ta EFCC ta kuwa ce rahotannin da suka samu na sirri sun tabbatar sun nuna cewa Idris ya kwashe kudaden ne ta hanyar tuntubar juna na bogi da kuma wasu ayyuka da suka sabawa doka ta hanyar amfani da wasu makusanta, da ‘yan uwa.
Hukumar ta ce an karkatar da kudaden ne ta hanyar zuba jari a Kano da Abuja.
Ta ce an kama Idris ne bayan ya gaza amsa gayyatar da hukumar ta yi masa domin amsa wasu tambayoyi kan zarge-zargen da suka shafi zamba.













































