A yau Laraba ne hukumar Alhazan Najeriya NAHCON, za ta fara jigilar maniyyata aikin hajjin bana zuwa ƙasa mai tsarki domin sauke farali.
Za’a ƙaddamar da fara jigilar maniyyatan bana ne a jihar Kebbi.
Tuni shugaban hukumar Alhazan ƙasar, Jalal Ahmed Arabi tare da wasu jami’an hukumar suka isa jihar, domin duba shirye-shiyen da hukumar ta yi gabannin fara jigilar maniyyatan.
Karin labari: “Za mu kafa kwamiti don binciken yadda aka mulki Ribas” – Fubara
NAHCON ta ce jirgin farko da zai tashi daga filin jirgin saman, Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi, zai ɗauki maniyyata 428.
Mataimakin shugaban Kasar Najeriya Kashim Shettima ne zai kasance babban baƙo a wajen bikin ƙaddamarwar, kamar yadda hukumar ta wallafa a shafinta na Facebook.
Karin labari: Yadda ake shigar da korafe-korafe ga Jami’an ‘Yan Sanda – Jami’i
Hukumar ta kuma ce tun a ranar Lahadi ne tawagar jami’an lafiya da manema labarai da masu kula da masaukai da kwamitin ciyarwa da sauran kwamitoci suka tashi zuwa ƙasa mai tsarkin don shirya fara shirye-shirye.
Hukumar alhazan ta ce za’a ci gaba da jigilar alhazan har zuwa ranar 10 ga watan Yuni.
Karin labari: Emefiele ya ce bashi da laifi kan buga bayanan kudi na Naira Miliyan 684 da Biliyan 18.96
NAHCON ta ce an zaɓi filayen jiragen sama 15 domin gudanar da jigilar maniyyatan na bana.
Kusan maniyyatan Najeriya 65,047 ne ake sa ran za su sauke farali a bana kamar yadda hukumar ta bayyana.