
A wani lamari mai ban al’ajabi da ya faru a lokacin sallar Asuba da sanyin safiyar ranar Laraba, Shafi’u Aminu mai shekaru 28 da haihuwa ya bankawa wani masallaci wuta da gangan a unguwar larabar Abasawa da ke karamar hukumar Gezawa ta jihar Kano.
A cewar wadanda lamarin ya rutsa da su, Aminu ya zuba mai a cikin masallacin, sannan ya kulle kofofin, inda ya kama masu ibada a ciki, lamarin da ya jefa al’umma cikin firgici da nuna rashin imani.
Sadik Kamal, daya daga cikin wadanda suka jikkata, ya ba da labarin abin da ya faru da shi.
Karin labari: NAHCON: za ta fara jigilar maniyyatan Najeriya zuwa Saudiyya
Kamal ya ce lokacin da wutar ta kama masallacin, ya yi kokarin tserewa amma ya ga kofar fita a kulle.
Ya bayyana cewa Aminu yana da tarihin tashin hankali a kauyen. A baya dai ya yi harbin kan mai uwa da wabi, inda ya yi barazana ga jama’ar kauyen, inda ya kara da cewa hukumomi sun taba kama shi tare da tura shi asibiti domin auna lafiyar kwakwalwarsa.
Wannan kone-kone na baya-bayan nan ba wani lamari ne da ya faru ba, kamar yadda Kamal ya ce, a baya Aminu ya kona motar dan uwansa tare da far masa.
Karin labari: Emefiele ya ce bashi da laifi kan buga bayanan kudi na Naira Miliyan 684 da Biliyan 18.96
Halayyar sa na rashin gaskiya ta haifar da damuwa a tsakanin mazauna kauyen, amma ba a dauki kwakkwaran mataki ba.
Ya kara da cewa ‘’Lokacin da gobarar ta tashi a lokacin sallar asuba, wadanda suka makara ne suka yi nasarar farfasa kofar tare da ceto wadanda suka makale a ciki.
Jaridar SolaceBase ta rawaito cewa kimanin masu ibada 29 ne suka samu munanan raunuka kuma an garzaya da su Asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.
Karin labari: Yadda ake shigar da korafe-korafe ga Jami’an ‘Yan Sanda – Jami’i
Zabiya Ibrahim, wacce ta shaida lamarin da abin ya shafi na ta, ta yi kira da a yi adalci. Ta jaddada cewa Aminu ya aikata da gangan ne babu wani tabin hankali a tattare da shi.
Ta ce, “Ya san yadda ake neman kudi,” in ji ta.
Ta na mai nuni da yadda ya shiga hawan wani mashahurin babur mai kafa uku wato (Adai-Adai Ta Sahu).
Zabiya ta bukaci gwamnati da ta tuhume shi da wannan aika-aikar.