Kano: Sagagi ya miƙa ragamar ma’aikatar kasuwanci ga Gwarzo, ya bayyana aikinsa a matsayin dama ta musamman

IMG 20260326 WA0164 750x430

Tsohon kwamishinan zuba jari, kasuwanci da masana’antu na jihar Kano, Gwani Shehu Wada Sagagi, ya miƙa ragamar ma’aikatar ga daraktan kasuwanci, Abubakar Bello Gwarzo, bayan cire shi daga mukaminsa da Abba Kabir Yusuf ya yi.

Miƙa ragamar wanda ya gudana a hedikwatar ma’aikatar ya nuna sauyin shugabanci a hukumance, bayan gwamnan ya umarci Sagagi da ya sauka daga mukaminsa a wani tsari da gwamnatin ta bayyana a matsayin sake fasalin gudanarwa.

Da yake jawabi ga manema labarai a wajen taron, Sagagi ya ce ya je ma’aikatar ne domin bin umarnin gwamnan na miƙa ragamar ma’aikatar ga babban jami’i mafi girma wanda shi ne daraktan kasuwanci, Abubakar Bello Gwarzo.

Sagagi ya bayyana lokacin da ya yi a kan mulki a matsayin wata dama ta musamman, yana mai cewa ya samu damar yi wa gwamnati aiki a muhimman mukamai guda biyu, na farko a matsayin shugaban ma’aikatan fadar gwamnati, daga bisani kuma a matsayin kwamishina.

Ya ce wannan dama ta ba shi ikon magance wasu matsaloli da ya daɗe yana gani a ma’aikatar, tare da yabawa daraktoci da ma’aikata kan goyon bayan da suka ba shi wajen aiwatar da manufofinsa.

Tsohon kwamishinan ya kuma gode wa gwamnan bisa damar da ya ba shi na yin aiki, tare da gode wa Allah da ya ba shi lafiya da ƙarfi wajen gudanar da aikinsa.

Ya ƙara da cewa barin mukami wani bangare ne na aikin gwamnati, yana mai cewa duk wanda aka naɗa dole ne ya shirya ranar da zai bar ofis.

A nasa jawabin, Gwarzo, wanda ya karɓi ragamar ma’aikatar, ya ce sauyin ya yi daidai da umarnin gwamnan, yana mai tabbatar da cewa ma’aikatar za ta ci gaba da aiki yadda ya kamata.

Ya ce za a yi ƙoƙarin tabbatar da tsari da ci gaba a ayyukan ma’aikatar tare da inganta harkokin ci gaba a jihar da ƙasa baki ɗaya.

Ya kuma gode wa jami’ai da baƙi da suka halarci taron, yana mai alƙawarin ci gaba da gudanar da ayyukan ma’aikatar bisa yadda gwamnati ke bukata.

Miƙa ragamar Sagagi ya biyo bayan cire shi daga mukami da gwamna ya yi, inda ya umarci a miƙa harkokin ma’aikatar nan take ga daraktan kasuwanci har sai an yi sabbin naɗe-naɗe.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here