Hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantu ta ƙasa JAMB ta sake kama wani da ake zargi da aikata damfarar jarrabawa mai suna Emmanuel Akataka, tare da cewa babu wani mutum ko ƙungiya da za su iya yin tasiri a sakamakon jarabawar UTME.
Magatakardar hukumar, Farfesa Is-haq Oloyede, ya bayyana hakan yayin da yake bayani ga manema labarai kan sake kama wanda ake zargin a Bwari da ke Abuja, inda ya yi gargadi ga ɗalibai da al’umma da su guji fadawa tarkon masu alkawarin ƙara maki ko taimako a jarrabawa.
Ya bayyana cewa irin waɗannan ikirari na damfara ne, yana mai cewa duk wanda ya shiga irin waɗannan harkoki na iya fuskantar asarar kuɗi da kuma matsalolin doka.
Ya ƙara da cewa wanda ake zargin ya taba kamuwa a baya bisa laifukan haɗa baki wajen aikata laifi, satar bayanan mutane, damfara ta internet da kuma wasu laifuka da suka shafi jarabawar UTME, inda ya yaudari akalla ɗalibai 94 ta hanyar karɓar kuɗi don ƙara musu maki.
Hukumar ta ba wa ɗaliban da abin ya shafa damar bayyana kansu domin tabbatar da rashin laifinsu, sannan da amincewar ma’aikatar ilimi ta tarayya aka soke rajistarsu, yayin da aka bayar da belin wanda ake zargin bisa tsarin doka.
Bayan samun belinsa, wanda ake zargin ya sake komawa yaudara ta hanyar tuntubar waɗanda ya taba damfara, inda ya sake karɓar kuɗi yana masu alkawarin hana soke rajistarsu, lamarin da ya kara nuna yadda ake amfani da dabarun damfara wajen cutar da ɗalibai.
Hukumar ta JAMB ta bayyana cewa za ta ci gaba da aiki tare da jami’an tsaro domin kamo duk masu aikata irin wannan laifi, tare da jan hankalin ɗalibai da iyaye da su bi hanyoyin da suka dace kawai, domin kare sahihancin tsarin jarrabawar ƙasa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa an miƙa wanda ake zargin ga hukumomin tsaro domin gurfanar da shi a gaban kotu.












































