Sojojin ƙasa a Najeriya sun yi ritayar manyan jami’ai 18 na rundunar samar da kayayyaki da sufuri ta sojojin ƙasa bayan kammala shekaru 35 suna hidima ga ƙasa.
Kamfanin dillancin labarai na ƙasa NAN ya rawaito cewa bikin sallamar wanda ya gudana cikin kayatarwa ya zo ne bayan kammala wani taron kwanaki uku da aka gudanar a birnin Benin, babban birnin jihar Edo.
Taron ya gudana ne ƙarƙashin taken inganta ƙarfin samar da kayayyaki da sufuri domin tabbatar da ingantaccen bayar da hidima ga ayyukan rundunar sojojin ƙasa a dukkan ayyukan da take gudanarwa.
Da yake jawabi a wajen bikin, kwamandan rundunar samar da kayayyaki da sufuri ta sojojin ƙasa, Manjo Janar Danjuma Shagaya, ya bayyana cewa jami’an da suka yi ritayar sun haɗa da manyan janarori huɗu da kuma brigediya janarori 14.
Ya bayyana cewa jami’an sun yi wa ƙasa hidima da sadaukarwa tun daga lokacin da aka ba su mukami har zuwa lokacin ritayarsu, yana mai cewa bikin wata hanya ce ta girmama gudummawar da suka bayar.
Ya ƙara da cewa wannan biki wata tsohuwar al’ada ce ta rundunar soji da ke ba da damar girmama shekaru na aiki da sadaukarwa ga ƙasa, tare da yabawa shugaban rundunar sojojin ƙasa kan aika wakili domin halartar taron.
Da yake magana a madadin waɗanda suka yi ritaya, Manjo Janar Olaniyi Dare ya bayyana cewa aikinsu ya shafe shekaru da dama inda suka yi wa rundunar sojojin ƙasa aiki a fannoni daban-daban na ayyukan soja, jagoranci da kuma ayyukan ofis.
Ya ƙara da cewa rundunar samar da kayayyaki da sufuri na taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da ingancin ayyukan rundunar sojojin ƙasa, musamman wajen samar da kayan aiki da tallafin sufuri ga sojoji a wuraren da ake gudanar da ayyuka a cikin ƙasa da wajen ta.












































