Sheikh Abduljabbar ya aika ƙorafi ga babbar jojin Najeriya kan hukuncin kisa da aka yanke masa, ya zargi hana shi ɗaukaka ƙara a shari’ar ɓatanci

Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara

Malamin addinin musulunci da ke Kano, Abduljabbar Nasiru Kabara, ya aika da ƙorafi ga babban alkaliyar Najeriya, mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, inda ya zargi hukumomin shari’a da na gwamnati da hana shi damar ɗaukaka ƙara kan hukuncin kisa da aka yanke masa bisa zargin ɓatanci.

A cikin wata wasiƙa mai shafuka 14 da kotun koli ta Najeriya ta karɓa a ranar 26 ga watan Maris, malamin ya bayyana hukuncin da aka yanke masa a matsayin rashin adalci da kuma abin da ya danganta da siyasa, yana mai cewa an yi hakan ne domin dakile shi.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa an same shi da laifi ne a wata babbar kotun shari’ar Musulunci a Kano a watan Disamba na shekarar 2022, inda aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya bisa kalaman da aka ɗauka a matsayin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW).

Bayan hukuncin, lamarin ya haifar da muhawara mai zafi a jihar, inda batutuwan addini ke haifar da ƙarfin ra’ayi daga jama’a, sannan aka mayar da shi zuwa gidan yari da ke Kuje.

A cikin ƙorafinsa, malamin ya bayyana cewa ƙoƙarin da ya yi na kalubalantar hukuncin ta hanyar kotunan ɗaukaka ƙara an hana su ci gaba, inda ya ce ya shigar da sanarwar ɗaukaka ƙara tun bayan hukuncin a 2022 tare da ƙarin buƙatu a shekarar 2024, amma ya zargi cewa an dakatar da shari’ar tare da sauya takardunsa.

Ya kuma zargi wasu alkalai da sauya ranaku da kuma karkatar da bayanansa ta hanyar da za ta amfanar da gwamnati, yana mai cewa duk wannan ya saba wa sashe na 38 na kundin tsarin mulkin Najeriya wanda ke ba da ‘yancin tunani, lamiri da addini.

Kabara ya ƙara da cewa matsalarsa ta fara ne bayan ya ƙi amincewa da wani shiri da ya ce wasu masu ƙarfi a Najeriya da ƙasashen waje suka ƙulla domin mayar da shi jagoran juyin juya hali na addini, inda ya ce an yi masa tayin kuɗaɗe masu yawa har zuwa Naira Miliyan 500 da kwangiloli amma ya ƙi.

Haka kuma ya zargi tsohon ministan ilimi Adamu Adamu da taka rawa a cikin lamarin, ciki har da aika jami’an tsaro domin kai farmaki gidansa da masallacinsa, tare da zargin haɗin baki tsakanin lauyoyin gwamnati da wasu jami’an shari’a wajen sauya takardun shari’ar.

Kabara ya roƙi babbar alkaliya ƙasar da ta shiga tsakani, yana mai cewa hukuncin kisa da aka yanke masa ya samo asali ne daga hukunci mai rauni, tare da gargadin cewa lamarin na nuna babbar matsala ta rashin adalci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here