
Karamin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle, ya bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yiwa Najeriya Addu’o’in samun zaman lafiya da tabbatar da tsaro.
Hakan na kunshe ne a cikin sakonsa na Eid-el Fitr mai dauke da sa hannun Mista Ahmad Dan-wudil, mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, wanda ya aikewa NAN a Abuja.
“Ganin wata yana nuna isar Eid el-Fitr.
Karin labari: Sarkin Musulmi ya bukaci al’umma su nemi Ilimi tare da yiwa shugabanni addu’a
“Yayin da muke bankwana da watan Ramadan mai albarka, bari mu rungumar Idi da budaddiyar zuciya da sabunta ruhi,” in ji shi.
Ya jaddada muhimmancin ci gaba da ayyuka masu kyau da aka kafa a cikin watan Ramadan mai alfarma.
Ya roki Allah da ya ba da dukkan alherin da ke cikin watan Ramadan.
Karin labari: Kotu ta saka ranar gurfanar da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da matarsa da wasu mutum 6
Ministan ya kuma yi addu’ar Allah ya kara wa kasa zaman lafiya da tsaro da wadata tare da jajirtattun sojojin Najeriya da ke fafutukar tabbatar da zaman lafiya da tsaron kasa.
Matawalle ya ci gaba da mika gaisuwar barka da sallah ga al’ummar musulmi tare da yi wa daukacin ‘yan kasar fatan zaman lafiya da annashuwa da kuma albarkar Idin karamar Sallah.