Tinubu ya bukaci ‘yan Najeriya su hada kansu don ciyar da kasar gaba

Tinubu Bola, najeriya, hada kai
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan kasar da su hada kansu da kuma nuna halin sadaukar wa, don gudanar da aikin gina kasar...

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci ‘yan kasar da su hada kansu da kuma nuna halin sadaukar wa, don gudanar da aikin gina kasar.

Karin labari: Eid El-Fitr: “Ku yi Addu’a don tabbatar da zaman lafiya da tsaro” – Ministan Tsaro

A cikin sakonsa na barka da Sallah da mai taimaka masa wajen hulda da kafafen yada labarai Ajuri Ngelale ya fitar, ya ce wannan lokaci ne na mai da lamura wajen Ubangiji, don haka ya kamata al’ummar kasar su dukufa wajen samar da hadin kai a tsakaninsu.

Karin labari: Sarkin Musulmi ya bukaci al’umma su nemi Ilimi tare da yiwa shugabanni addu’a

Shugaba Tinubu wanda ya taya al’ummar Musulmin Najeriya da ma duniya baki daya murya, ya kuma yi addu’ar Allah ya amshi ibadun da suka gabatar, kamar yadda jaridar BBC Hausa ta wallafa.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here