Sarkin Musulmi ya bukaci al’umma su nemi Ilimi tare da yiwa shugabanni addu’a

Sarkin Musulmi, ilimi, shugabanni, addu'a
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli na Harkokin Addinin Musulunci ta kasa (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ja hankalin al’ummar...

Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli na Harkokin Addinin Musulunci ta kasa (NSCIA), Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya ja hankalin al’ummar Musulmi da su himmatu wajen neman ilimi don karfafa imaninsu.

A sakonsa na Sallah a ranar Laraba, Abubakar ya jaddada muhimmancin ci gaba da yi wa shugabanni addu’a da kuma ci gaban kasa.

“Ya kamata mu nuna godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba mu kyautar rai da lafiya, wanda ya ba mu damar gudanar da azumin kwanaki 30 da yin bukukuwan Eid-el-Fitr.

Karin labari: Kotu ta saka ranar gurfanar da tsohon gwamnan Kano Abdullahi Ganduje da matarsa ​​da wasu mutum 6

“Yau babbar rana ce a addinin Musulunci yayin da al’ummar Musulmi a fadin duniya ke bikin cikar watan Ramadan da bukukuwan Sallah.

“Bugu da kari, mu dawwamar da ruhin tausayawa da taimakon juna, kamar yadda aka yi a cikin watan Ramadan, tare da ba da taimako ga mabukata,” in ji shi.

Sarkin Musulmi ya yabawa gwamnatin jihar Sokoto karkashin jagorancin Gwamna Ahmed Aliyu bisa jajircewa da hadin kai da malaman addinin Musulunci suke yi wajen ganin an samu hadin kai.

Karin labari: Fitacciyar jarumar Kannywood, Saratu Gidado Daso ta rasu tana da shekara 56

Ya kuma yaba da kokarin gwamnati na tallafawa marasa galihu da ma’aikatan gwamnati, da tabbatar da tsaro da ci gaban jihar.

A halin da ake ciki, Gwamna Ahmed Aliyu ya bukaci al’ummar Musulmin jihar da su ci gaba da gudanar da ibadar watan Ramadan domin samun rahama da gafarar Allah.

Aliyu, a sakonsa na Sallah ga al’ummar Musulmi bayan kammala azumin watan Ramadan na 2024, ya roki masu hannu da shuni da su ci gaba da nuna tausayi da karamci ga marasa galihu domin samun albarka.

Karin labari: Gwamnan Kano ya sake nada Imam Ogan Boye mukaminsa

“Ina sane da dimbin ayyukan taimako da wasu ’yan kasarmu masu hannu da shuni ke bayarwa ga mabukata a cikin al’ummarmu, wanda a hakika abin a yaba ne.

“A namu bangaren, gwamnati ta ware makudan kudade don tallafawa marasa galihu a fadin jihar,” in ji shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here