Fitacciyar jarumar Kannywood, Saratu Gidado Daso ta rasu tana da shekara 56

Saratu Daso

Shahararriyar Jarumar Kannywood, Saratu Gidado Daso ta rasu tana da shekara 56

Wata majiya daga dangin ta shaida wa SOLACEBASE cewa fitacciyar jarumar ta rasu ne da sanyin safiyar Talata a Kano.

Za a yi jana’izarta a yammacin yau da karfe 4:00 na yamma, kamar yadda majiyar ta bayyana.

Saratu wadda aka haifa a ranar 17 ga watan Junairun shekarar 1968 ta kasance fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finan Hausa ta kusan shekaru ashirin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here