Gwamnan Kano ya sake nada Imam Ogan Boye mukaminsa

Gwamnan, Kano, mukaminsa, ogan boye
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake nada Yusuf Imam (Ogan Boye), wanda ya kore shi daga mukaminsa saboda kalaman batanci ga mataimakin shugaban...

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya sake nada Yusuf Imam (Ogan Boye), wanda ya kore shi daga mukaminsa saboda kalaman batanci ga mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima.

Gwamnan ya sallami Imam Imam a matsayin mai ba shi shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni a watan Satumbar da ta gabata tare da kwamishinan filaye da tsare-tsare, Adamu Aliyu, wanda ya yi barazanar kisa ga alkalan kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar.

Gwamnatin ta ce ra’ayoyin da jami’an biyu suka bayyana ba su wakiltar matsayin gwamnatin jihar karkashin Gwamna Yusuf.

Karin labari: Ba’a ga watan sallah a Najeriya ba

Bayan watanni takwas, an sake nada mutanen biyu. Yayin da aka sake nada Aliyu a watan Maris, an sake kiran Imam a watan Afrilu.

Mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature, a ranar Talata, ya sanar da cewa an sake nada Imam zuwa ofishinsa na baya.

A cewar kakakin gwamnan ya kuma amince da nadin wasu karin mashawarta na musamman da sauran shugabannin hukumomin gwamnati.

Karin labari: Emefiele ya ki amsa wasu sabbin tuhume-tuhumen da ake masa

Ibrahim Barde, Farfesa an nada shi mai ba da shawara na musamman kan harkokin kudaden shiga (IGR) da Abdulhamid Danladi mai ba da shawara na musamman kan harkokin kasashen waje sannan Bello Kiru ya zama mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa.

Sauran wadanda aka nada sun hada da Nura Shanono, wanda ya koma daga mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa zuwa Manajan Daraktan Hukumar Injiniya da Gina Ruwa (WRECA).

Karin labari: ‘Yan ta’adda sun kashe masu aikin sa kai na tsaro su 30 a jihar Neja

Baba Umar ya kuma koma ne daga mai ba da shawara na musamman ga babban sakataren gudanarwa na hukumar kula da cibiyoyi masu zaman kansu da na sa kai.

An nada Nasir Muhammad Darakta Janar na Kanana da Matsakaitan Masana’antu (SMEs) yayin da Aminu Bako zai zama Mataimakin Manajan Daraktan Hukumar Noma da Raya Karkara ta Kano (KNARDA).

An nada Mukhtar Yusuf a matsayin mataimakin Manajan Daraktan Hukumar Injiniya da Gine-gine ta Ruwa (WRECA).

Mista Bature ya ce nadin ya fara aiki nan take.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here