Emefiele ya ki amsa wasu sabbin tuhume-tuhumen da ake masa

Emeifele, sabbin, tuhume-tuhume, efcc, cbn
Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya musanta zargin da ake masa. An gurfanar da shi ne a babban kotun Ikeja bisa zarginsa...

Tsohon gwamnan babban bankin Najeriya CBN, Godwin Emefiele, ya musanta zargin da ake masa.

An gurfanar da shi ne a babban kotun Ikeja bisa zarginsa da laifin cin zarafi da kuma karkatar da biliyoyin daloli.

Alkalin kotun shi ne Justice Rahman Oshodi.

An karanta tuhume-tuhumen guda 26 ga Emefiele da wanda ake tuhumarsa, Henry Omoile.

Karin labari: Da Dumi-Dumi: Majalisar dokokin jihar Edo ta tsige mataimakin gwamnan jihar Philip Shaibu

Sai dai duka wadanda ake tuhumar sun musanta aikata dukkan laifukan.

Wadanda ake tuhumar sun nemi a bada belinsu har sai an saurari karar da kuma yanke hukunci.

Godwin Emefiele dai ya bukaci kotu ta bayar da belinsa na musamman kan yadda ake tuhumarsa da sauraron karar da kuma yanke hukunci kan shari’ar ko kuma a sake shi ga lauyansa har sai an yanke hukunci.

Karin labari: Sojoji sun saki sunayen manyan ‘yan ta’adda da suka kashe

Lauyan sa, Lebi Lawal ya ce ya kamata kotu ta duba matsayinsa.

Lauyan ya ce “Shekaru tara, Emefiele ya kasance ma’aikacin banki na daya a Najeriya”.

Lauyan ya kuma bukaci kotun da ta duba halin Emefiele tun bayan kama shi.

“Jastis Muazu ya bayar da belin Emefiele kuma yana halartar shari’ar da ake yi masa a babban kotun tarayya da ke Abuja.

Karin labari: Sojin Najeriya sun bayyana dalilin sakin ‘yan ta’addan gwamnatin Borno

Tun lokacin da aka bayar da belinsa bai taba rasa ranar sauraron sa ba, kuma masu gabatar da kara sun kusa kammala tattara shari’ar.

Wanda ake tuhuma ya kasance a ko da yaushe yana gabatar da kansa a gaban kotu domin amsa tuhumar da ake masa,” in ji lauyan.

“A ranar Alhamis din da ta gabata ne EFCC ta kira shi ya ce an gurfanar da shi a gaban kotu, kuma ya sake gabatar da kansa a gaban kotu a yau domin amsa tuhumar da ake masa.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here