Dan takarar gwamna a jam’iyyar APC a Jihar Gombe, Isa Ali Ibrahim Pantami, ya janye daga shiga zaben fidda gwanin gwamna a jam’iyyar da aka shirya gudanarwa a ranar 21 ga Mayu, inda ya danganta hakan da zargin keta dokar Zabe ta 2026 da rashin gaskiya a tsarin.
Pantami ya sanar da janyewar ne a cikin wata sanarwa da Barrista Ibrahim M. Attahir ya fitar a ranar Talata a madadin Pantamiyya Movement, yana mai cewa an yanke shawarar ne sakamakon damuwa kan abin da ya kira rashin gaskiya da gazawar jami’an jam’iyyar wajen bayar da mahimman bayanai don gudanar da zaben fidda gwani mai inganci.
Sanarwar ta ce tsohon ministan ya shiga neman takarar ne bayan bukatun shugabannin siyasa, matasa, mata da sauran masu ruwa da tsaki a jihar, kuma ya cika dukkan sharuda da tsarin da jam’iyyar ta gindaya.
Ta kara da cewa wasikun da kungiyar lauyoyinsa suka aike wa sassa masu alaka na jam’iyyar don neman bayani kan tantance wakilai, tsarin kada kuri’a da wuraren tattara sakamako ba a amsa su ba, duk da maimaita bukatar da suka yi.
Pantami ya kuma zargi akwai rashin gaskiya a zaben fidda gwani na kai tsaye na Majalisar Kasa a APC da aka yi a baya-bayan nan a Gombe, yana mai cewa an sanar da sakamako ba tare da an gudanar da zabe a wasu wurare ba, wani lamari da ya ce ya jefa shakka kan ingancin zaben fidda gwanin gwamna da aka shirya gudanarwa a 21 ga Mayu.
Ya gode wa magoya bayansa, musamman matasan da suka ba da gudummawa domin siyan fom din sha’awar yin takara, da kungiyoyin mata, masu gudanarwa da mambobin Pantamiyya Movement bisa goyon bayansu.
Sanarwar ta ƙara da cewa kungiyar za ta sanar da matakan siyasa na gaba a lokacin da ya dace, tare da rokon magoya baya da su ci gaba da kasancewa cikin kwanciyar hankali da bin doka.












































