Yanzu-Yanzu: EFCC ta kama tsohon Ministan Lantarki da aka yanke wa hukunci

Mamman

Hukumar Yaki da Masu yi wa Tattalin Arziki Kasa Ta’annati (EFCC) ta kama tsohon Ministan Wutar Lantarki, Saleh Mamman, wanda a kwanakin baya Kotun Tarayya da ke Abuja ta yanke wa hukuncin dauri kan almundahana da kudi gwamnati a lokacin da yake kan wannan mukami.

Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ne ya tabbatar da kama shi da misalin karfe 3:30 na safiyar Talata.

An kama shi a Kaduna tare da wasu mutum biyu da ke kare shi, gidan da aka kama shi a yanzu ana bincike a kai shi.

Kotun ta same shi da laifi a dukkan tuhume-tuhume 12 da EFCC ta gabatar masa. A ranar 13 ga Mayu ne aka yanke wa Mamman hukunci da daurin shekara 75 a gidan gyaran hali a zaman kotun da bai halarta ba kan zargin karkatar da Naira 33.8 biliyan da ke da alaka da ayyukan samar da wutar lantarki na Zungeru da Mambilla.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here