![Sojoji sun saki sunayen manyan 'yan ta'adda da suka kashe Sojojin, Najeriya, sunayen, kwamandojin, 'yan ta'adda, kashe](https://solacebasehausa.com/wp-content/uploads/2024/04/Sojojin-Najeriya-696x464.jpg)
Hedikwatar tsaro, a ranar Alhamis, ta fitar da sunayen manyan kwamandojin ‘yan ta’adda da aka kashe a hare-hare daban-daban a yankin arewacin kasar.
DHQ ta yi nuni da cewa an kashe kwamandojin ‘yan ta’addar ne a wasu hare-hare daban-daban tsakanin watan Janairu zuwa Maris na shekarar 2024.
Sunayen manyan ‘yan ta’addan su ne Abu Bilal Minuki (aka Abubakar Mainok) – Shugaban lardin Is-Al Furqan (ISGS da ISWAP) da Haruna Isiya Boderi. Ya kasance wani dan ta’adda da yayi kaurin suna a dajin Birnin Gwari a jihar Kaduna da kuma babbar hanyar Abuja ta Kaduna.
Karin labari: Gwamnan Kano ya kaddamar da kwamitin da zai bincike da kwato kadarorin gwamnati
Sojoji sun kashe shi a ranar 21 ga watan Fabrairun 2024.
Sauran sun hada da Kachallah Damina, dakaru sun kashe shi a ranar 24 ga watan Maris.
An kashe shi tare da mayaka sama da 50, Kachallah Alhaji Dayi, da Kachallah Idi (Namaidaro), sai Kachallah Kabiru (Doka), da Kachallah Azarailu (Farin-Ruwa), da kuma Kachallah Balejo da wasu da dama.
Karin labari: Muna Da Tabbaci Gwamna Yusuf Zai Ciyar Da Kano Gaba – NAWOJ
Daraktan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba ne ya bayyana wa ‘yan jarida sunayen yayin wani taron tattaunawa a Abuja.
Ya kara da cewa, an kashe ‘yan ta’adda 2,351, yayin da aka kama 2,308, sannan an kubutar da mutane 1,241 da aka yi garkuwa da su a tsawon lokacin da aka yi garkuwa da su.