Gamayyar Kungiyar ‘yan jaridu mata ta kasa NAWOJ ta bayyana kwarin gwiwa kan salon mulkin gwamnan kano Engr Abba Kabir Yusuf wajan ciyar da kano gaba.
Shugaban kungiyar ta kasa Hajia Aisha Ibrahim ce ta bayyana haka yayin liyafar shan ruwa da gwamnatin kano ta shiryawa ‘ya’yan kungiyar.
Yayin liyafar, shugabar kungiyar wadda ta sami wakilcin sakatariyar kungiyar yan jaridu mata ta kasa Hajia Wasila Ibrahim Ladan, tace tana tabbaci gwamna Yusuf na kokari matuka wajan fitoda sabbin manufofin ciyar da jihar kano gaba.
“E gaskiya la’akari da irin manufofi da tsare tsaren sa, muna da tabbaci kwalliya za ta biya kudin sabulu” Inji Wasila Ladan
Yayin liyafar kungiyar yan jaridun mata ta gabatar da shaidar yabo ga gwamnan kano Engr Abba Kabir Yusuf bisa irin shirye shiryen da yake aiwatar wa don ciyar da kano gaba.
Daganan Ladan ta godewa Gwamna Yusuf bisa karrama su wajan shirya irin wannan kasaitacciyar liyafar shan ruwa la’akari da muhimman su ga cigaban kasa.
Tunda farko da ya maida jawabi, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana farin ciki bisa kokari da kungiyar keyi wajan cigaban kasa dakuma hadin kan dasuke bayarwa a sauran tsaren gwamnati domin samun nasara.
Gwamna Yusuf daganan yayi alwashin cigaba da tallafawa kungiyar ta hanyoyin dasuka dace akokarin zaburar da kungiyoyin mata na shiga sabgogi da tsare tsaren gwamnati don damawa dasu.
“Hakika nayi farin ciki matuka yadda allah swt ya nuna mana wannan rana damuke shan ruwa tareda wannan kungiya mai daraja, kungiyar yan jaridu mata, ina yaba muku, kuma ina kira gareku daku tsaya tsayin daka kan irin tsare tsaren dakuke kai” Inji Gwamna Yusuf
Hakanan Gwamnan Yusuf ya bayyana jin dadi kan yadda kungiyar ke aiwatar da shirye shiryen ta cikin tsari kuma su ka dace.
Taron liyafar shan ruwan ya sami halattar manyan jami’an gwamnati dasuka hadar da mataimakin gwamna kuma kwamishin kananan hukumomi alh Aminu Abdussalam Gwarzo, da kwamishinan yada labarai Baba Halilu Dan-tiye, shugaban gidan rediyon kano Alhaji Abubakar rano da ‘yan sauran tawaga.
#End: