‘Bani da tarihin aikata laifi ko kadan’ – Shugaban Miyetti Allah dake tsare.

leader of the Miyetti Allah Kautal Hore Bello Badejo

Shugaban kungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da ake tsare da shi, Bello Bodejo, ya shaidawa babbar kotun tarayya da ke Abuja cewa ba shi da wani laifi. Bodejo, wanda aka kama kuma ake tsare dashi a kan zargin aiki da ‘yan bindiga, ya shaida wa mai shari’a Inyang Ekwo cikin wata bukatar neman belin da lauyansa Ahmed Raji, SAN ya shigar.

A cikin karar mai lamba: FHC/ABJ/CR/141/2024 da aka gabatar ranar 28 ga Maris, ya nemi a ba shi belinsa bisa sharuddan sassaucin har sai an saurari karar da aka yanke ma sa.

Bodejo, wanda aka kama a ranar 23 ga watan Janairu a Malia, jihar Nasarawa, kuma yana tsare a hannun hukumar leken asiri, an gurfanar da shi a gaban mai shari’a Ekwo a ranar 22 ga watan Maris.

Da yake bayar da wasu dalilai tara da zai sa a bada belinsa, shugaban kungiyar Miyetti Allah da ke tsare ya ce shi bashida ko da tarihin aikata wasu laifukan da ake tuhumarsa da su.

“Wanda ake tuhuma ba shi da wani tarihin aikata laifuka,” in ji shi.

A cewarsa, shurar dayayi dakuma shaharar sa, ba zai tsallake sharuddan neman beli ba idan an aminta da wannan bukata.

Wanda ake kara, wanda ya yi alkawarin kasancewa a kan lokaci wajen halartar shari’ar da ake yi masa, ya ce a shirye yake ya bayar da wadanda za su tsaya masa kamar yadda kotu ta bukata.

Sai dai a wata takardar kara da Noma Wando, magatakarda a ma’aikatar shari’a ta tarayya ya shigar, ya nemi da ayi watsi da bukatar da Bodejo ya shigar.

Ya ce Bodejo yana fuskantar shari’a kan laifukan da suka shafi ta’addanci dake barazana ga tsaron kasa da lafiyar jama’a.

Jami’in ya yi zargin cewa Bodejo ya kuma ba da tallafin kayan aiki, taimako da sufuri don ayyukan da suka shafi irin waɗannan ayyukan da suka saba wa Sashe na 29, 2 (3) (g} (xii) da 12 (a) da Sashe na 2 (3) (g)(xii) ), da kuma 13 (2) (b) na Dokar Ta’addanci, 2022.

Ya ce bayan gurfanar da shi kotu, kotu ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi a cibiyar leken asiri, inda ta bayar da umarnin a gaggauta saurarar karar tare da tsawaita shari’ar daga ranar 27 zuwa 30 ga Mayu.

Abubakar ya ki amincewa da cewa shugaban kungiyar Miyetti Allah da aka tsare zai tada wata barazana idan ba a bayar da belinsa ba.

Yayin cigaba da sauraran karar lauyan da ya gurfana a gaban Bodejo, Dokta Sulaiman Usman, SAN, ya shaida wa kotun cewa suna da bukatar neman belin wanda ake sauraron kara kansa.

Babban Lauyan ya ce za su bukaci karin lokaci don mayar da martani kan sabbin batutuwan da aka gabatar a cikin takardar shaidar.

Lauyar mai shigar da kara, Y. A Imana, bai yi suka kan wannan roko da Usman yayi na ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here