Gwamnatin tarayya ta bada tabbacin samar da isassun kudade domin kamala aikin manyan titunan gwamnatin tarayya da suka hada da ta Gombe zuwa Biu a Borno da sauran hanyoyin da za su inganta tattalin arziki a fadin kasar nan.
Babban Sakatare na Ma’aikatar Ayyuka da Gidaje ta Tarayya, Mista Hassan Musa, ne ya bayar da wannan tabbacin a Abuja, yayin da yake jawabi ga shugaban kwamitin kasafin kudi na majalisar wakilai, Mauktar Betara.
Shugaban ya samu rakiyar Ahmadu Usman Jaha da Kabir Tukura a ziyarar aiki a ma’aikatar.
Musa ya shaida wa ’yan majalisar cewa ma’aikatar ta samar da karin kudade na hanyar Gombe zuwa Biu.
A cewar sa, majalisar zartaswa ta tarayya za ta amince da hanyar tare da wasu zababbun hanyoyin gwamnatin tarayya a fadin kasar domin kammalawa.
“A madadin shugaban kasa Muhammadu Buhari da minista, Mista Babatunde Raji Fashola, ina so in tabbatar da cewa mun samu Karin wasu kudade na wannan hanyar kuma za a ba dan kwangilar duk wani abin da ya dace don aiwatar da shi.
“bugu da kari a yanzu muna da damar samar da kudade wanda zai ba su damar biyan su nan da nan an kammala ayyukan,” in ji shi.
Musa ya yabawa ‘yan majalisar kan ziyarar aiki da suka kai ma’aikatar, inda ya ce ta ba da damammaki wajen yin mu’amala da kuma bayar da rahoto kan abubuwan da ma’aikatar ta yi.
Ya yi alkawarin ma’aikatar ta himmatu wajen ganin ta cimma burinta na inganta Najeriya da ci gabanta.
Tun da farko, Betara wanda ya jagoranci tawagar ya jaddada bukatar samar da wasu kudade na hanyar Gombe zuwa Biu.
Betara wanda ya nuna damuwarsa kan halin da hanyar ke ciki duk da kasafin kudin shekara wanda ya ce bai wadatar ba.
“Abin da ya kawo ni da yammacin yau, na zo ne saboda babbar hanyar mu – titin Gombe-Biu.
“An bayar da kwangilar ne kimanin shekaru shida da suka gabata, kuma dan kwangilar yana tafiyar hawainiya a aikin.
“A duk lokacin da muka tattauna da shi, matsalarsa ita ce kudade, domin ba za a iya samun kudaden gudanar da irin wannan aiki ta hanyar kasafin kudi ba.
“Saboda haka na yanke shawarar zuwa na ga sakatare na dindindin da minista don in roke su, kuma na yi farin ciki a yau, domin an sanar da ni cewa akwai dama don tallafawa aikin hanyar Gombe zuwa Biu a kasar nan,” inji shi.
Dan majalisar ya ce a mako mai zuwa zai gana da ‘yan kwangilar bayan amincewar majalisar zartarwa ta tarayya domin ci gaba da gudanar da ayyukan. (NAN)










































