Kungiyar CAJA ta nemi tallafin masu ruwa da tsaki domin samarwa al’ummar Kano ci gaba  

IMG 20231203 WA0172 750x430
IMG 20231203 WA0172 750x430

Wata kungiyar farar hula mai suna CAJA ta kaddamar da wani sabon shiri mai taken “Karfafa Gwiwar Matasa don Inganta Ci gaban Jama’a a Jihar Kano”.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa a karkashin wannan shiri, kungiyar ta CAJA ta kaddamar da wata tawagar jakadu 75 wadanda za su sanya ido tare da yin hulda da zababbun jami’an gwamnatin jihar Kano.

Da yake jawabi a wajen taron da aka gudanar ranar Lahadi a Kano, babban daraktan hukumar ta CAJA, Kabiru Saidu Dakata, ya ce shirin na da nufin tunawa zababbun jami’an da suka yi alkawuran da suka dauka a lokacin yakin neman zabe.

Dakata ya ce aikin zai kuma baiwa zababbun ‘yan majalisa kwarin gwiwar kafa wa da kula da ofisoshin mazabu a kowace mazaba, da kuma hada kai da jama’arsu yadda ya kamata.

A cewarsa, gidauniyar MacArthur ce ta tallafa wa shirin ta hannun Asusun Tallafawa Matan Najeriya.

A nasa jawabin kwamishinan raya karkara da ci gaban al’umma, Alhaji Hamza Safiyanu Kachako, ya yabawa kokarin kungiyar ta CAJA bisa wayar da kan jama’a tare da inganta tsarin dimokuradiyya a fadin jihar.

A nasa bangaren, shugaban Jakadun Dimokuradiyya, Aminu Muktar Isa Wudil, ya ce za su yi iya kokarinsu wajen inganta harkokin jama’a a Jihar Kano, kuma ba za su baiwa kungiyar ta CAJA kunya ba.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here