Rundunar yan sanda a jihar Bauchi ta ce, adadin wadanda suka mutu sakamakon turmutsitsin sadaka da aka yi a Bauchi a ranar Lahadi ya kai bakwai.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, SP Ahmed Wakil, ya ce wasu mata uku sun mutu.
Rahotanni sun ce an tattake wasu mutane hudu har lahira a ranar Lahadin da ta gabata a wani yunkurin su na karbar sadaka a kamfanin Shafa Holdings Plc da ke hanyar Jos a Bauchi a jihar Bauchi.
Karin karatu: Ƴansanda a jihar Bauchi sun kama wani matashi kan zargin kashe mahaifiyarsa da taɓarya
Rundunar ‘yan sandan ta ce lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:20 na safe a lokacin da kamfanin ke gudanar da zakka na shekara-shekara wanda aka fi sani da sadaka, domin taimakawa marasa galihu a jihar.
“Likitan da ke asibitin koyarwa na Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa (ATBUTH) ya tabbatar da cewa karin wasu mata biyu sun mutu a asibitin daga cikin wadanda aka kawo domin jinya.
“Dayar matar danginta ne suka kai ta gida, amma ta mutu a gida,” in ji Wakil.
Wata shaida, Laraba Saleh, ta ce wasu mutane da dama, mata da kananan yara sun samu raunuka yayin turmutsitsin.
(NAN)










































