Wuta ta cinye direban mota da yaronsa a gidan mai

Tanker explosion New 750x430

An tabbatar da mutuwar mutane biyu a wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Talata a kofar Orita Challenge da ke gidan man GABSTAB a Ibadan.

A wata sanarwa da babban manajan hukumar kashe gobara ta jihar Oyo, Yemi Akinyinka ya fitar, ya ce wani direban tankar mai tare da yaronsa sun rasa rayukansu a lamarin.

Akinyinka ya ce hukumar kashe gobara ta tura jami’anta zuwa wurin da lamarin ya faru a lokacin da suka samu labarin gobarar da misalin karfe 5:15 na safe.

Karin karatu: Gobarar Dambatta: Gwamnatin Kano ta yi alkawarin tallafawa wadanda abin ya shafa

“Mun samu bayanai game da gidan mai na GABSTAB Mega, Orita Challenge, gobara da ta tashi da karfe 5:15 na safe kuma muka tura mutanenmu nan take, sai dai tuni Direban da yaron motar sun kone kurmus,” in ji shi.

Sai dai babban manajan ya ce an shawo kan gobarar, kuma daga baya za a yi karin bayani kan lamarin. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here