Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya jajantawa ‘yan uwa, abokan arziki, da makusantan marigayi Abdussalam Abdullateef, wanda har zuwa rasuwarsa, ya kasance mai ba da shawara na musamman kan harkokin Yarabawa.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a ranar Litinin.
A baya dai jaridar SolaceBase ta bayar da rahoton rasuwar marigayi Abdussalam Abdullateef ranar Asabar bayan gajeriyar jinya.
Labari mai alaƙa: Mai baiwa Gwamna Yusuf shawara na musamman ya rasu
A ziyarar ta’aziyyar da Gwamna Yusuf ya kai gidan marigayin da ke unguwar Jaba a karamar hukumar Ungogo, ya jagoranci tawagar gwamnati domin jajantawa iyalan mamacin.
Har ma ya bayyana rasuwar Abdussalam a matsayin babban rashi, ba ga iyalansa kadai ba, ga daukacin al’ummar jihar Kano da Najeriya baki daya.
Gwamnan ya yabawa sadaukarwa da gaskiya, da jajircewar marigayi mashawarcin nasa na samar da hadin kai da ci gaba a jihar.
Ya kuma bayyana irin gagarumar gudunmawar da ya bayar wajen karfafa huldar tsakanin al’umma da kuma ciyar da muradun al’ummar Yarabawa a Kano.
Gwamna Yusuf ya yi addu’ar Allah ya jikansa da rahama.